Yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza ta fara aiki da safiyar yau, kamar yadda rundunar sojin Isra’ila ta sanar.
A cikin sa’o’i 72 ne ake sa ran sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a musayar fursunonin Falasdinu.
Tunda farko dama gwamnatin Isra’ila ta sanarda amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da Hamas, wadda Amurka ta jagoranta.
Yarjejeniyar za ta kai ga sakin dukkanin yan Isra’ila da aka yi garkuwa da su lokaci guda, A madadin haka, Isra’ila za ta saki Falasdinawa kusan 2,000.
Yarjejeniyar na zuwa ne bayan shafe shekara biyu ana yaki.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana matakin a matsayin wani muhimmin ci gaba.