Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, a gefen wani taro a kasar Tajakisatan da yake halatta a kasar ya bayyana ce firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya fada masa cewa ya isar da sakonsa ga gwamnatin JMI kan cewa yana son a warware matsalolin da ke tsakaninsa da JMI cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.
Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya bayyana shugaba shugaban yana son yazama mai tsaga tsakani a rikicin da JMI take yi da HKI da kuma hukumar maikula da makamashin Nukliya ta duniya wato IAEA, a dai dai lokacinda yake kiyaye dangantakarsa ta diblomasiyya da kasashen biyu. Putin ya kara da cewa ya sami sakonni daga HKI kan cewa mu fadawa Tehran HKI bata bukatar fito na fito da ita. Dangane da hukumar IAEA kuma putin ya ce: shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya Rafeal Grossi ya bayyana cewa ya san cewa JMI tana son warware matsalolin da ke tsakanin hukumarsa da ita, sai har yanzu akwai matsalolin da ba’a warware ba kan shirin makamashin nukliyar kasar, amma yana ganin ana iya warwaresu idan har an cimma yarjeniya tsakanin bangarorin biyu.
Daga karshe Putin ya ce a ganinsa abokansa Iraniyawa a shirye suke su warware matsalolin da ke tsakaninsu sannan a sake farfado da dangantaka da hukumar IAEA. A cikin watan Yunin da ya gabata ne HKI da Amurka suka kaiwa JMI hare-hare da nufin kifar da gwamnatin kasar da kuma lalata cibiyoyinta na makamashin Nukliya.