Falasdinawan da HKI ta kora daga gidajensu a birnin Gaza sun kama hanyar komawa gidajensu a birnin Gaza dake arewacin yankin
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa ya zuwa tsakiyar rana a yau jumm’a sojojin HKI sun janye makamansu daga babban titi wanda ya taso daga arewacin zirin Gaza zuwa kudancin yankin , wanda kuma ake kira Titin Rasheed. Sun janye zuwa inda aka amince zasu koma a wannan matakin na sabon yarjeniyar. Hotunana daga yankin ya nuna falasdinawa gungu-gungu suna takawa da kafa zuwa arewacin zirin Gaza, daga inda sojojin yahudawan suka koresu a farkon watan da ya gabata, suka kuma hana kowa bin kan titin Rasheed.
A wani bangare kuma gwamnatin HKI ta fara bayyana sunayen Falasdinawa wadanda suke tsare da su, saboda musayarsu da fursinoni yahudawa wadanda Hamas take tsare da su. Wanda yake yake da cikin shirin. Yahudawan sun bayyana sunayen falasdinawa 25 wadanda suke cikin wadanda za’a saka. Yahudawan sun bayyana cewa daga cikin sunayen babu Marwan Barguthe da kuma Ahmad Saadat, manya-manyan falasdinawa wadanda suka fi shekaru 40 yahudawan suna tsar da su.
Ana saran na da sa’o’ii 72 za’a saki fursinoni yahudawa 48 wadanda suke tsare a hannun kungiyar Hamas, tare da falasdinawa kimani 2000 da yahudawan zasu saka.