Kungiyar RSF Ta Shigar Da Kara A Kotun ICC Kan Kisan Isra’ila A Gaza.

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar yan jarida da bata da iyaka a karon na biyar ta shigar da kara a babban kotun duniya mai hukumta laifukan yaki ICC kan kisan da HKI take yi wa yan jaridu a bakin aikinsu a yankin gaza. A ranar talata ce aka sanar da sake shigar da karar,tun bayan […]
Kasar Pakistan Tayi Gwajin Makami Mai Linzami Na Fatah 4 Cikin Nasara.

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Pakistan sun bayyana cewa sun yi gwajin makami mai linzami na fatah 4 da aka kara inganta shi, wanda zai iya kai hari mai nisan kilomita 750 ba tare da wani kuskure ba, wanda ya kara inganta karfin makamai masu linzami na kasar. Babbar nasarar da aka samu […]
A gobe Ne Ake Sa Ran Tawagar Agaji Ta Sumud Flotilla Za ta Isa Gaza.

Rima hassan wani bafranshe mai nuna goyon bayan falasdinu kuma mamba a majalisar tarayyar turai kuma daya daga cikin tawagar Sumud flotilla ya sanar ta kafar sada zumunta cewa gobe ne ake saran tawagar flotilla za ta isa yankin Gaza duk da yake cewa Isra’ila ta tanadi tsauraran matakai na tunkararta. A daren jiya ma […]
Iran Ta yi Kira Da A Gaggauta Kakabawa HKI Takunkumi

Jakadan Iran na dindin a majalisar dinkin duniya yayi kira da a gaggauta kakabawa HKI takunkumi saboda hujjoji da ake da shi dake tabbatar da cewa tana kisan gillan ne kan alumma Gaza, kuma yayi tir da matsayin kasashen turai game da abin da ke faruwa a yankin gaza. A baya bayan nan kwamitin bincike […]
A yau Najeriya ke bikin cika shekaru 65 da samun yancin kai

Yau Najeriya ke cika shekaru 65 da samun ƴancin kai daga Turawan mulkin mallaka, inda aka saba gudanar da bukukuwa da kuma nazari dangane da ci gaban da ƙasar ta samu a ƙarƙashin mulkin ƴan ƙasa da kuma ƙalubalen da take fuskanta. Bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da jama’ar ƙasar ke […]
Aragchi: Za’a Fara Tattaunawa Ta Karshe Dangane Da Shirin Snapback

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi ya bayyana a jiya Talata kan cewa yana dab da fara tattaunawa ta karshe dangane da shirin Snapback wanda ya maida takunkuman tattalin arziki na MDD kan kasar bayan daukewa na shekaru 10. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka a birnin […]
Tinubu: Na Gaji Rusashen Tattalin Arziki A Sanda Na Karbi Ikon Kasar

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, a jawabin da ya gabatarwa yan Najiya a safiyar yau Laraba daya ga watan Octoban shekara ta 2025, ya bayyana cewa a lokacinda ya karbi shugabancin kasar daga thohuwar gwamnati tattalin arzikin kasar tamkar ya rushe, amma ya kara dacewa, an wuce mafi munin halin. Shugaban ya bayyana haka […]
Iran: Dakarun Ruwa Na Iran A Shirye Suke Su Shiga Yaki Da Kowa Don Kare Kasa

Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdurrahim Musawi yay aba da shirin sojojin ruwan kasar na fuskantar duk wani harin da makiya zasu kawowa kasar daga yanzun, Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Musawi yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda ya kai ziyarar aiki a sansanin sojojin ruwa […]
Pezeshkiya: Aiki Ta Kasar China Yana Da Matukar Muhimmanci Musamman A Wannan Halin Da Ake Ciki

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa aiwatar da yarjeniya ta musamman da kasar china a halin da ake ciki a yankin da kuma yadda duniya take sauyawa da sauri ya zama wajibi ga kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacin da yake gabatar […]
Tawagar Jiragen ‘Assumud’: Yahudawan Isra’ila Sun Kai Mana Hare-Hare Da Safe

Tawagar jiragen ruwan ‘Usturah’ masu rajin karya kofar ragon da aka yiwa Gaza, sun bada labarin cewa sojojin ruwa na HKI sun kai masu hare-hare a safiyar yau Laraba. Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta bayyana cewa, majiyar ta bayyana cewa al-amarin akwai hatsari amma duk da haka zasu ci gaba da hanyarsu ta zuwa Gaza, […]
Shahadar Nasrallah Ta Gadar Da Juriya A Kan Gwagwarmaya Ga Al’ummomi Masu ‘Yanci

Shekara guda bayan shahadar Sayyed Hassan Nasrallah, yanayin siyasa da zamantakewar yankin ya sake yin tasiri da tunawa da shi. Nan da nan kuma shahadarsa ta zama wani muhimmin batu na samun hadin kai a tsakanin kungiyoyi masu adawa da mamaya da kuma sabunta himma ga manufofin tsayin daka. Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar […]
Muhammad ElBaradei Ya Yi Kakkausar Suka Ga Shirin Trump Akan Gaza

Tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa,Muhammmad El-Baradei ya ce, Shirin na Trump akan Gaza ba komai ba ne sai kokarin tilasta larabawa su mika wuya, su kuma rusuna. Muhammad El-Baradei ya wallafa a shafinsa na X cewa; na saurari taron manema labaru a fadar White House akan Gaza, amma na fada cikin […]
Trump Ya Bayar Da Umarnin Aike Wa Da Jiragen Ruwa Na Nukiliya Zuwa Kusa Da Rasha

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fada a jiya Talata cewa ya bayar da umarnin aikewa da jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa dake dauke da makaman Nukiliya da su karaci gabar ruwan kasar Rasha, a matsayin kandagarko. Trump ya kara da cewa; A cikin kwanakin bayan an aiko mana sakon barazana daga Rasha, […]
Gaza: ‘Yan Gwagwarmaya Suna Ci Gaba Da Kai Wa Sojojin Mamaya Hare-hare

Kungiyoyin gwgawarmaya na Hamas da Jihadul-Islami sun sanar da kai hari akan sojojin HKI da suke yin kutse a cikin yankin Gaza’ Rundunonin soja na “Al-Kassam” na Hamas da ‘Sarayal-Qudus” na Jihadul-Islami sun ce sun kai hare-haren ne akan sojojin mamayar da su ka shiga cikin yankunan Arewa da kudancin Gaza. A jiya Talata dakarun […]
Sojojin Yemen Sun Kai Hari Akan Wani Jirgin Ruwa Da Ya Nufi HKI

Sojojin na Yemen sun sanar da kai hari wani jirgin ruwa mai suna: MINERVAGRACHT’ saboda ya keta dokar hana zuwa tasoshin jiragen ruwan Falasdinu dake karkashin mamaya. Janar Yahya Sari ne ya yi wannan sanarwa yana mai kara da cewa; An kai harin ne akan ruwan tekun Aden ta hanyar amfani da wani makami mai […]