Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fada a jiya Talata cewa ya bayar da umarnin aikewa da jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa dake dauke da makaman Nukiliya da su karaci gabar ruwan kasar Rasha, a matsayin kandagarko.
Trump ya kara da cewa; A cikin kwanakin bayan an aiko mana sakon barazana daga Rasha, don haka na aike da jiragen ruwa masu makaman Nukiliya da shi ne makamai mafi hatsari.”
Shugaban kasar na Amurka ya riya cewa kasarsa tana gaba da kasashen Rasha da China da ci gaban shekau 25 a fagagen kimiyya dakuma kera jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa.”