Sojojin Yemen Sun Kai Hari Akan Wani Jirgin Ruwa Da Ya Nufi HKI

Sojojin na Yemen sun sanar da kai hari wani jirgin ruwa mai suna: MINERVAGRACHT’ saboda ya keta dokar hana zuwa tasoshin jiragen ruwan Falasdinu dake

Sojojin na Yemen sun sanar da kai hari wani jirgin ruwa mai suna: MINERVAGRACHT’ saboda ya keta dokar hana zuwa tasoshin jiragen ruwan Falasdinu dake karkashin mamaya.

Janar Yahya Sari ne ya yi wannan sanarwa yana mai kara da cewa; An kai harin ne akan ruwan tekun Aden ta hanyar amfani da wani makami mai linzami, ya kuwa shafi jirgin ruwan kai tsaye, yana kuma Shirin nutsewa.

Kakakin sojojin Yemen din ya bayyana harin da cewa an kai shi ne saboda taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta da yi wa kisan kiyashi.

Haka nan kuma ya ce za su ci gaba da kai hare-hare akan duk wani jirgin ruwa wanda ya yi kokarin zuwa HKI ta hanyoyin ruwan tekun “Red-Sea” tare da yin gargadi ga kamfanonin jiragen ruwa da su kiyaye.

Sojojin Yemen dai sun shiga cikin masu taya Falasdinawa fada tun bayan  da HKI ta shelanta yaki da kisan kiyasa akan al’ummar Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments