Tinubu: Na Gaji Rusashen Tattalin Arziki A Sanda Na Karbi Ikon Kasar

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, a jawabin da ya gabatarwa yan Najiya a safiyar yau Laraba daya ga watan Octoban shekara ta 2025, ya

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, a jawabin da ya gabatarwa yan Najiya a safiyar yau Laraba daya ga watan Octoban shekara ta 2025, ya bayyana cewa a lokacinda ya karbi shugabancin kasar daga thohuwar gwamnati tattalin arzikin kasar tamkar ya rushe, amma ya kara dacewa, an wuce mafi munin halin.

Shugaban ya bayyana haka ne lokacinda yake gabatar da jawabin ranar samun yencin kai karo na 65. Ya kuma bayyana cewa ya gabatar da sauye sauyen da dama wadanda suka sa al-amura suka fara komawa kamar yadda yakamata.  Daga ciki ya ce cire tallafin man fetur mai cike da cin hanci da rashawa, ya taimaka wajen rage barnan da akewa tattalin arzikin kasar. Ya ce: Mun zabi jin dadin gobe, kan walwala na yau..

Shugaban ya ce mummuna halin da mutanen shuka shiga a farkon daukar wadan nan matakan sun fara sauki. Saboda an tsallak halin mafi munin da gyran yake bukata.

Dangane da matsalolin tsaron da kasar take fuskanta kuma shugaban ya bayyana cewa yana tare da wadanda abin ya shafa don tabbatar da tsaro a duk fadin kasar, kuma jami’an tsaron kasar suna iya kokarinsu don ganin ta kare mu daga yan ta’adda da masu satar mutane da kuma dukiyoyimmu.

Yace an sami ci gaba a harkokin tsaro a gabaci da kuma arewa maso gabacin kasar. Haka ma a arewa maso yammacin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted