Kasar Pakistan Tayi Gwajin  Makami Mai Linzami Na Fatah 4 Cikin Nasara.

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Pakistan sun bayyana cewa sun yi gwajin makami mai linzami na fatah 4 da aka kara inganta shi, 

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Pakistan sun bayyana cewa sun yi gwajin makami mai linzami na fatah 4 da aka kara inganta shi,  wanda zai iya kai hari mai nisan kilomita 750 ba tare da wani kuskure ba, wanda ya kara inganta karfin makamai masu linzami na kasar.

Babbar nasarar da aka samu wajen gwajin makamai mai linzami da aka kara inganta shi acikin gida na fatah 4,wanda aka karfafa shi da wani tsari na zamani,  makamin zai iya kaucewa harin makami mai linzami na makiya ta hanyar tsarin rungumar kasa yayin da yake kai hari,

Wannan wani bangare ne na karfin sojin kasar kuma da sannu za su kara inganta karfin makami mai linzami na fatah 4, inda zai kara  dogon zangon da yake ci, kadamar da shirin ya samu halartar babban hafsan hafsoshin sojin kasar ta Pakistan, da kwararrun masana kimiya da injiniyoyin.

Shugaban kasa da pira ministan pakistan da kuma shugaban kwamitin hadin guiwa da ma’aikata sun taya mahalarta wajen kaddamarwar murna na gwada da makami mai linzami na fatah 4 cikin gagarumar nasara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments