Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar yan jarida da bata da iyaka a karon na biyar ta shigar da kara a babban kotun duniya mai hukumta laifukan yaki ICC kan kisan da HKI take yi wa yan jaridu a bakin aikinsu a yankin gaza.
A ranar talata ce aka sanar da sake shigar da karar,tun bayan harin 7 ga watan oktoba da isra’ila ta kaddamar a yankin gaza, inda ta kai hari kan yan jarida 30 daga watan mayu na 204 zuwa Augustan shekara ta 2025 ta kashe 25 daga ciki ta jikkata wasu gida biyar kuma.
Darakatan sadarwa na kungiyar ta RSF Antoine bernard ya bayyana cewa isra’ila a koda yaushe tana kokari ne wajen rufe bakin yan jarida,
Yace yana kira ga ICC ta dauki mataki duk da barazana da matsin lamba da takunkumi da take fuskanta, kuma tayi aikinta , tayi aikinta kawai dole ne a hukumta wadanda ke kashe yan jarida
Akwai Fatima Hassouna yar shekaru 25 da haihuwa yar jarida ce an kasheta ne tare da wasu danginta guda 10 har da wata yar uwarta mai dauke da juna biyu, mai suna Alaaa a wani hari da isra’ila ta kai a ranar 16 ga watan Aprilun shekara ta 2025.