Kungiyoyin gwgawarmaya na Hamas da Jihadul-Islami sun sanar da kai hari akan sojojin HKI da suke yin kutse a cikin yankin Gaza’
Rundunonin soja na “Al-Kassam” na Hamas da ‘Sarayal-Qudus” na Jihadul-Islami sun ce sun kai hare-haren ne akan sojojin mamayar da su ka shiga cikin yankunan Arewa da kudancin Gaza.
A jiya Talata dakarun na Kassam sun watsa sanarwar a shafinsa na “Telegram’ da a ciki ya kunshi cewa, sun kai hare-haren ne akan ‘yan mamaya a kusa asibitin Jordan da kudancin unguwar “Tal Hawa” a kudancin birnin Gaza.
Haka nan kuma rundunar ta Kassam ta ce ta kai wani harin akan motar soja da ta shiga cikin wata makaranta ta ” Rahibatul-Wurdiyyah” dake Tallul-Hawa.”.
Har ila yau dakarun na Hamas sun ce, sun yi fada gaba da gaba da sojojin HKI tare da kashe da kuma jikkata adadi mai yawa.
Bugu da kari sun tarwatsa wata tankar yaki ta “Mirkava” ta hanyar dasa mata abubuwa masu fashewa.
An ga jiragen sama masu saukar angulu sun sauka a yankin domin daukar gawawwaki da wadanda su ka jikkata.
Ita kuwa rundunar ” Sarayal-Qudus” ta jihadul-Islami ta sanar da kai nata hare-haren ne akan sojojin mamaya a arewacin birnin Gaza.
Haka nan kuma sun yi amfani da makamai mai linzami samfurin GBU da ‘yan mamaya su ka bari a Gaza, tare da tarwatsa shi akan sojojin HKI a kan titi na 8 dake kudancin Gaza. A can ma an ga jirgin sama mai saukar Angulu yana jigilar wadanda su ka jikkata da halaka.