Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa aiwatar da yarjeniya ta musamman da kasar china a halin da ake ciki a yankin da kuma yadda duniya take sauyawa da sauri ya zama wajibi ga kasar Iran.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacin da yake gabatar da sakon murna ga gwamnatin kasar China kan cika shekaru 76 da kafuwar kasar. Wanda kuma itace ranar kasa a kasar ta China.
Pezeshkiyan ya kara da cewa wannan ranar ta samuwar kasar China, rana ce da hadin kai da ci gaba da kuma godewa ga irin ci gaban da kasar ta samu daga lokacin zuwa yanzu a cikin gida da kuma fagen kasa da kasa.
Shugaban ya bayyana cewa a haduwarsa ta karshe da shugaba XI ya jaddada masa amfanin muhimmancin aiwatar da dukkan yarjeniyoyin da fahintar juna da suka cimma da kasar ta China, saboda muhimmancin hakan ga kasar Iran da kuma ita China. Daga karshe ya karfafa cewa kasashen biyu zasu ci gaba da karfafa dangantaka a tsakaninsu tare da mutunta juna da kuma girmamaw