Muhammad ElBaradei Ya Yi Kakkausar Suka Ga Shirin Trump Akan Gaza

Tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliya  ta kasa da kasa,Muhammmad El-Baradei ya ce, Shirin na Trump akan Gaza ba komai ba ne sai kokarin tilasta larabawa

Tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliya  ta kasa da kasa,Muhammmad El-Baradei ya ce, Shirin na Trump akan Gaza ba komai ba ne sai kokarin tilasta larabawa su mika wuya, su kuma rusuna.

Muhammad El-Baradei ya wallafa a shafinsa na X cewa; na saurari taron manema labaru a fadar White House akan Gaza, amma na fada cikin damuwa mai tsanani akan halin da Gaza take ciki da kuma makomarta, haka nan kasashen larabawa baki daya.”

Tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa ya kuma ce; Wannan Shirin ba komai ba ne, sai na neman a mika wuya a kuma rusuna, ba shiri ne na neman zaman lafiya ba.”

Har ila yau, ya kuma yi suka akan yadda shugaban na kasar Amurka bai ambaci wahalhalun da Falasdinawa suke ciki ba a yayin jawabin da ya yi a MDD.

Shirin na Amurkan dai ya kunshi nada tsohon fira ministan Birtaniya Tony Blair a matsayin wanda zai jagoranci hukumar da za a kafa a Gaza. Haka nan kuma yin kira ga Hamas da ta mika makamanta na gwgawarmaya, sannan kuma ta saki dukkanin Fursunonin yakin da ke hannunta. Sai idan an yi hakan ne HKI za ta saki fursunonin Falasdinawa da suke zaman kurkuku na har abada, ta kuma fara janyewa sannu a hankali daga wuraren da ta mamaye a cikin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments