Tawagar Jiragen ‘Assumud’: Yahudawan Isra’ila Sun Kai Mana Hare-Hare Da Safe

Tawagar jiragen ruwan ‘Usturah’ masu rajin karya kofar ragon da aka yiwa Gaza, sun bada labarin cewa sojojin ruwa na HKI sun kai masu hare-hare

Tawagar jiragen ruwan ‘Usturah’ masu rajin karya kofar ragon da aka yiwa Gaza, sun bada labarin cewa sojojin ruwa na HKI sun kai masu hare-hare a safiyar yau Laraba.

Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta bayyana cewa, majiyar ta bayyana cewa al-amarin akwai hatsari amma duk da haka zasu ci gaba da hanyarsu ta zuwa Gaza, duk tare da wadannan hattsurran.

Labarin ya kara da cewa, jirgin Alman, ya gamu da hare-hare daga yahudawan wanda ya tilasta masa jada baya zuwa wani waje. Banda ya an yanke dukkan kafafen sadarwa da waje.

Gwamnatin yahudawan dai sun sha alwashin hana dukkan jiragen Ustura isa gaza, kuma ta bayyana cewa ta tura jiragen ruwan yaki, wadanda suka kama dukka mutanen da suke cikin kananan kwale-kwale zuwa cikin wani jirgin ruwa yaki tare da tsaresu a ciki har zuwa lokacinda za’a san abinda za’a yi da su.

Sojojin yahudawa sun bayyana cewa idan ta kama zasu nutsar da wasu jiragen ruwan da suke tahowa Gaza. Kuma mai yuwa wasu su rasa rayukansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments