Aragchi: Za’a Fara Tattaunawa Ta Karshe Dangane Da Shirin Snapback

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi ya bayyana a jiya Talata kan cewa yana dab da fara tattaunawa ta karshe dangane da shirin Snapback

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi ya bayyana a jiya Talata kan cewa yana dab da fara tattaunawa ta karshe dangane da shirin Snapback wanda ya maida takunkuman tattalin arziki na MDD kan kasar bayan daukewa na shekaru 10.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka a birnin NewYork na kasar Amurka, a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa tattaunawarsa da babban sakataren MDD Antonio Gutterres kan shirin na Snapback shi ne na karshe.

Ya ce a tattaunawar zai gabatarwa Guttres matsayin kasar Iran kan wannan matakin da kasashen E3 suka dauka a kan kasar Iran. Yace wannan ya nuna irin ketan da wadan nan kasashe sukewa JMI da kuma kiyayyar da suke nuna mata.

Ministan ya bayyana cewa ya gudanar da taron da kasashe da kungiyoyi kimani 31 a gefen taron babban zauren MDD dangane da al-amuran tattalin arziki.

Yace taron China na ‘Global Initiative’ yana da matukar muhimmanci dangane da tattalin arzikin kasashen da suke cikin shirin, Iran tana ciki.

Banda haka ministan ya bayyana cewa ya tattauna tare da sauran kasashen da suka sanyawa yarjeniyar JCPOA hannu, tattaunawa mai zurfi dangane da shirin Snapback wanda wadanan kasashe suka sake mayarwa kan Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments