Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce dole ne dukkan kasashen duniya su yi kokarin kawo karshen laifukan da Isra’ila ke aikatawa a zirin Gaza da kuma kawo karshen killacewa da take yi wa yankin.
Pezeshkian ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake karbar takardar shaidar sabbin jakadun kasashen Habasha, Estonia, Djibouti, Laos, Cambodia, Burundi, Latvia, Myanmar, da Nepal.
Ya ce gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da kara zafafa laifukan da take aikatawa a kan al’ummar Palastinu marasa kariya da ake zalunta a zirin Gaza.
Shugaban na Iran ya jaddada cewa: Dole ne dukkan kasashen duniya musamman kasashen musulmi su kara himma da hadin gwiwa wajen dakile wadannan laifuka a Gaza, da kuma isar da taimako mai yawa ga mutanen Gaza.
Ya yi gargadin cewa wani “mummunan bala’i” yana faruwa a Gaza, inda Isra’ila ke kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, tare da toshe hanyoyin samun abinci, ruwa, da magunguna da sunan kare kai.
“Babban abin bakin ciki shi ne ana aikata wadannan laifuka a kan idanun wadanda ke da’awar kare hakkin bil’adama, dimokuradiyya, da ‘yancin dan adam a duniya,” in ji Pezeshkian.
Yakin Isra’ila, wanda ya fara a watan Oktoban 2023, ya yi sanadin shahadar Falasdinawa akalla 61,430 tare da jikkata sama da 153,213.