Mali: An Kama Sojoji Fiye da 40 Bisa Zargin Yunkurin Juyin Mulki

Sojojin Kasar Mali kimani 45 aka kama biyu daga cikinsu masu mukamin Janar a karshen makon da ya gabata a kokarin da suka yi na

Sojojin Kasar Mali kimani 45 aka kama biyu daga cikinsu masu mukamin Janar a karshen makon da ya gabata a kokarin da suka yi na juyin mulki a kasar

Shafin yanar gizo na labarai ;Afrika News: ya bayyana cewa daga cikin wadanda aka kama har da janar Abass Dembele, kuma tsohon gwamna na lardin Tsakiyar Mopti. Majiyoyi kusa da Abbas sun bayyana cewa sojoji sun kama shi ne a safiyar ranar lahadi a wajen birnin Bamako babban birnin kasar, ba tare da wani karin bayani ba.

Har’ila yau labarin ya kara da cewa, Nema Sagara, mai mukaman brigadier General a sojojin sama na kasar, kuma mace wacce ba wanda ya fita mukami a sojojin kasar tana daga cikin wadanda aka kama.

Firai ministan kasar ya bayyana cewa dukkan wadanda aka kama sojoji ne a kasar .Tun watan Augustan shekara 2020 ne kanar Assimi Goita ya jagoranci juyin mulki a mali wanda ya kawo karshen democeadiyya a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted