Kashi 3/4 na kasashe mambobi a majalisar dinkin duniya sun amince da samar da kasar Falasdinu, mai zaman kanta tare da kasar Australia a yau Litinin ta bada sanarwan cewa zata shelanta amincewarta da kasar Falasdinu a matsayin mai zaman kanta a taron babban zauren mdd wana za;a gudanar a cikin watan Satumba mai zuwa.
Shafin labarai na yanar gizo, Arab News na kasar saudiya ya bayyana cewa, yakin da kungiyar Hamas ta fara da HKI a ranar 7 ga watan octoban shekara ta 2023 ya jawowa Falasdinawa tausayi a mafi yawan kasashen duniya in banda ita HKI da kuma Amurka.
Wadan nan kasashe sun yi Imani kan cewa Palasdinawa zasu sami yenci ne kawai a kan teburin tattaunawa. Sai dai HKI da Amurka basu amince da samuwar kasar Falasdinu ba, kuma yana da ra’ayin cewa HKI kasashe karama, yakamata ta kwace wasu kasashen larabawa don fadada kasar.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana cewa cikin kasashe 193 na MDD kasashe 145 sun amince ko zasu amince da samuwar kasar falasdinu daga cikin har da kasashen faransa, Canada da burtraniya.
sai gwamnatin kasar Iran wacce tafi ko wace kasa a cikin kasashen musulmi taimaka Falasdinwa, ta yi imanin cewa Amurka da kuma HKI ba zasu taba amincewa da kasar Falasdinu sai tare da amfani da karfi.