Kwamitin Tsaro ya yi zaman gaggawa kan Shirin Isra’ila na mamaye Gaza

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zaman gaggawa a hedikwatar MDD da ke birnin New York a jiya Lahadi, bayan matakin da

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zaman gaggawa a hedikwatar MDD da ke birnin New York a jiya Lahadi, bayan matakin da majalisar ministocin Isra’ila ta dauka na fadada ayyukan soji da kuma mamaye yankin zirin Gaza.

Mataimakiyar  Sakatare-Janar mai kula da harkokin Turai, Tsakiyar Asiya da Amurka, Miroslav Jenča, ta jaddada a yayin zaman  cewa, “ba za a iya dakatar da dimbin wahalhalun jin kai da ake fama da su a Gaza ba, sai ta hanyar tsagaita bude wuta nan take kuma mai dorewa,” tana mai kira da a gaggauta sakin dukkan fursunoni ba tare da wani sharadi ba.

Jenča ta yi kira ga Isra’ila da ta bi abin da ya rataya a wuyanta a karkashin dokar jin kai ta kasa da kasa, ta ba da damar isar da kayan agaji cikin gaggawa kuma cikin aminci, ba tare da tsangwama ko kawo cikas ga wanann shiri ba, da kuma barin isar da kayan ga jama’a, tana mai jaddada bukatar “kare fararen hula, gami da ma’aikatan jin kai da masu neman taimako.”

A nasa bangaren, wakilin Aljeriya a MDD Ammar Benjamaa ya ce Isra’ila ba ta damu da dokokin kasa da kasa ko kuma bil’adama ba, ya kara da cewa “Isra’ilawa suna nuna rashin tausayi, Rashin Imani da dabi’a na dabbanci, suna kawar da Palasdinawa daga matsayinsu na yan Adam tare da kaskantar da su zuwa matsayin dabbobi kamar yadda suke gani.”

A martanin da ta mayar, wakiliyar Amurka ta dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Dorothy Shea, ta dora alhakin dukkanin abin da Isra’ila take aikatawa a kan Hamas.

Dangane da matakin da Isra’ila ta dauka na Shirin mamaye  Gaza, ministocin harkokin wajen kasashen Australia, Jamus, Italiya, New Zealand, da Birtaniya sun sanar da kin amincewa da matakin na Isra’ila, tare da jaddada aniyarsu ta bai daya wajen aiwatar da yarjejeniyar kafa kasashe biyu ta hanyar yin shawarwari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments