Sojojin Mamayar Isra’ila Sun kai Wasu Munanan Hare-Hare Kan Yankunan Zirin Gaza

Sojojin mamayar Isra’ila sun harba wata mugunyar ‘karfin wuta’ da jiragen saman yaki kan yankin kudancin Gaza Bayan tsakar dare ne jiragen yakin sojojin haramtacciyar

Sojojin mamayar Isra’ila sun harba wata mugunyar ‘karfin wuta’ da jiragen saman yaki kan yankin kudancin Gaza

Bayan tsakar dare ne jiragen yakin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kaddamar da luguden wuta a kudancin birnin Gaza.

Cibiyar yada labaran Falasdinu ta nakalto majiyoyin da ta bayyana a matsayin na cikin gida na cewa: Jiragen saman sojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da hare-haren wuce gona da iri, inda suka harba makamai masu linzami sama da 20 cikin ‘yan mintuna a kudancin mahadar Al-Musalaba da Dawla da kuma kusa da masallacin Ali, inda suka nufi kudu.

Wakilin cibiyar ya ruwaito cewa, galibin hare-haren sun fi karkata ne a kan titin 8 da ke kudancin Gaza.

Wadannan hare-haren dai na zuwa ne a daidai lokacin da barazanar da sojojin mamaya ke yi na kaddamar da wani gagarumin farmaki a kan birnin na Gaza ke kara ta’azzara, da nufin kwace iko da birnin da kuma raba mazauna birnin da tilastawa kauracewa gidajensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments