Israila Ta Kashe ‘Yan Jarida 4 A Harin Da Ta Kai Kan Tantinsu A Gaza

‘Yan jarida 4  Anas al-Sharif da Mohammad Qraiqea, da masu daukar hoto Mohammad Nawfal da Ibrahim Daher sun shahada a wani harin da Haramtacciyar Kasar

‘Yan jarida 4  Anas al-Sharif da Mohammad Qraiqea, da masu daukar hoto Mohammad Nawfal da Ibrahim Daher sun shahada a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai kan wani  tantin ‘yan jarida a arewacin zirin Gaza.

Anas al-Sharif, shahharen dan jarida wanda ya sha bayar da rahotonnai da suke fallasa ayyukan kisan kare dangi da Isra’ila take aikatawa kan fararen hula a Gaza, lamarin da ya Sanya sojojin Isra’ila farautar rayuwarsa.

A baya Isra’ila ta bayyana cewa Anas mamba ne na kungiyar Hamas kuma kwararre a bangaren makaman kungiyar, a kan yana daga cikin wdanda take dako.

Kwamitin Kare ‘Yan Jaridu (CPJ) ya fitar da wata sanarwa a ranar 24 ga Yuli, 2025, inda ya ce al-Sharif na fuskantar wani kamfe na karya da nufin halasta rayuwarsa daga bangaren  sojojin Isra’ila.

Kungiyar kare hakkin ‘yan jarida ta CPJ ta kara da cewa, “Kwamitin Kare ‘Yan Jaridu ya damu matuka game da yadda Isra’ila take dakon rayuwarsa bisa wasu zarge-zarge na karya marasa tushe balantana makama.

“Hukumar ta IDF ta yi ikirarin cewa da yawa daga cikin ‘yan jaridar da aka kashe da gangan a Gaza ‘yan ta’adda ne, ciki har da ma’aikatan Al Jazeera hudu – Hamza Al Dahdouh, Ismail Al Ghoul, Rami Al Refee, da Hossam Shabat.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted