Kwamitin Tsaron MDD Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar Isra’ila A Kan Gaza

Kasashen Turai biyar na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya sun ki amincewa da matakin mamaye Gaza Wakilin dindindin na Slovenia ya gabatar da wata sanarwa

Kasashen Turai biyar na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya sun ki amincewa da matakin mamaye Gaza

Wakilin dindindin na Slovenia ya gabatar da wata sanarwa ga kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a madadin Burtaniya, Faransa, Denmark, da Girka, yana mai cewa: “A matsayinsu na kasashen Birtaniya, Denmark, Faransa, Girka, da Slovenia, sun kira taron gaggawa na kwamitin tsaron Majalisar kan halin da ake ciki a Gaza. Suna Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na fadada ayyukanta na soji a Gaza. Ya kuma jaddada cewa: Hakan yana barazana tare da keta dokokin kasa da kasa, yana mai kiran gwamnatin mamayar Isra’ila da ta hanzarta janyewa daga wannan matsayi.

 Ya jaddada cewa: Duk wani matakin mamaye yankunan Falasdinawa da gwamnatin mamayar Isra’ila zata yi yana matsayin keta dokokin kasa da kasa kuma fadada ayyukan soji a yankin zai wurga rayukan fararen hula cikin hatsari, ciki har da rayukan fursunonin yahudawan sahayoniyya da suke hannu ‘yan gwagwarmaya.

Har ila yau, kungiyar agaji ta Red Cross ta yi gargadin cewa: Ana fama da yunwa a Gaza, kuma yara na mutuwa saboda yunwa. Yunwa ta kai wani matsayi mai tsananin gaske wanda fararen hula masu matsananciyar wahala ke jefa rayuwarsu cikin kasada a wuraren raba kayan agaji domin ciyar da iyalansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted