Iran: Ba a yanke wani abu game da tattaunawa da Washington ba

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa “babu wani abu da aka yanke ya  yanzu game da tattaunawa da Amurka,” ya kara

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa “babu wani abu da aka yanke ya  yanzu game da tattaunawa da Amurka,” ya kara da cewa “babu wani tabbci kan zabar wata kasa da za ta karbi bakuncin tattaunawar.”

A jawabin da ya yi a gefen taron majalisar ministocin a jiya Lahadi, Araqchi ya yi jawabi kan  ziyarar mataimakin babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA wanda ke shirin isa birnin Tehran a yau litinin.

Araqchi ya bayyana cewa “babu wani shiri na ziyartar wata tashar nukiliya kafin a cimma wata matsaya kan hakan,” ya kara da cewa wannan tsarin “zai dogara ne kan dokar majalisar dokokin kasar Iran kawa,” kuma “ba za a fara wasu ayyuka na hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar IAEA ba har sai majalisar ta fayyace matsayin haka a bisa dokar kasa.”

Bugu da kari, Araqchi ya yi nuni da cewa, ana ci gaba da tuntubar juna tsakanin kasarsa da kasashen Turai, inda ya kara da cewa, sun tabo batun mayar da takunkumin da aka kakaba mata wanda aka dauke bayan cimma yarjejeniyar nukiliya a  shekarar 2015.

Araghchi ya bayyana cewa matsayin Iran kan shawara da  Turai shi ne cewa, Iran  Ba a daukar kasashen Turai a matsayin wani bangare a cikin yarjejeniyar nukiliya, amma dai a halin yanzu  masana daga bangarorin biyu suna tattaunawa kan batutuwa da suka shafi bangaren fasaha ne kawai ba kan sauran batutuwa na yarjejeniyar nukiliya ba.

A wani bangaren kuma a jiya ne Allah ya yi wa fitaccen masani kan zane-zane a kasar Iran Mahmud Farshian rasuwa, ya shahara da zane-zane masu ni da abubuwa na addini da tarihi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments