Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Kai Wa Masu Neman Agaji Hare-hare A Gaza

Adaidai lokacin da yakin Gaza yake cika kwanaki 653 ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; yunwa ta kashe Falasdinawa 900, daga cikinsu da akwai kananan yara 71.  Haka nan kuma sanarwar ta ce da akwai wasu falasdinawan 6,000 wadanda suke fama da yunwa, suke neman abinda za su ci. A cikin kisan […]

Fiye Da Mutane 1000 Ne Aka Kashe A  Rikicin Yankin Suwaida Na Kasar Syria

Cibiyar dake kula da kare hakkin bil’adama a kasar Syria, 9 almirsad) ta fitar da bayani akan rikicin da ya tashi a yakin Suwaida, inda ta bayyana cewa adadin wanda su ka rasa rayukansu sun wuce 1000 a cikin mako daya kawai. Bayanin ya ce, an kashe  mayakan Duruz 336, sai fararen hularsu 298. Haka […]

Admiral Musawi: An Sake Sabbin Na’urorin Tsaron Sararin Samaniyar Iran

Mataimakin kwamandan sojojin Iran mai kula da tsara farmaki Admiral Mahmud Musawi ya bayyana cewa: Mun yi nasarar samar da sabbin na’urori tare kuma tsofaffin da ake da su, da suke iya yi wa ilahirin samaniyar Iran rumfa daga kowane irin hari na makiya.” Admiral Musawi ya yi ishara da nasarorin da sojojin jamhuriyar musulunci […]

Pezeshkiyan Ya Ce: Iran Ba Zata Mika Kai Ga Bukatun Amurka Ba

A lokacinda yake tabbatar da cewa shirin makamashin Nukliya na kasar Iran na zaman lafiya ne wanda dukkan wadanda yakamata su san hakan sun sani, to Iran ba zata saurarawa duk wani matsi kan shirin ba don biyan bukatun wasu. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a lokacin […]

Firaministan Australia ya soki harin Isra’ila kan masu neman agaji a  Gaza

Firayim Ministan Australia Anthony Albanese ya yi kakkausar suka  game da ayyukan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a Gaza, yana mai kiran rahotannin kashe Falasdinawa a lokacin da suke cikin layin  neman abinci da ruwan sha, tare da bayyana cewa wannan ba abu ne da za a iya karewa da kowace irin hujja ba. A wata hira […]

‘Yan tawayen M23 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin Congo

‘Yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta nan take da gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a kasar Qatar a wannan Asabar, kamar dai yadda wani jami’i da ke da masaniya kan tattaunawar ya tabbatar wa kafofin yada labarai. Tsagaita wutar wani bangare ne na ayyana ka’idojin da […]