Masu Fafutuka Na Amurka Sun Yi Zanga-Zanga A Brooklyn Don Neman Kawo Karshen Ta’addanci A Gaza

Masu fafutuka na Amurka sun yi zanga-zanga a Brooklyn don neman kawo karshen ta’addanci a Gaza Dubban masu fafutuka ne suka halarci wani gagarumin tattaki

Masu fafutuka na Amurka sun yi zanga-zanga a Brooklyn don neman kawo karshen ta’addanci a Gaza

Dubban masu fafutuka ne suka halarci wani gagarumin tattaki na lumana a Sunset Park da ke Brooklyn, birnin New York, karkashin taken “A tsagaita wuta Yanzu.” Mahalarta taron sun gudanar da kiran neman kawo karshen yakin Gaza cikin gaggawa da kuma kawo karshen goyon bayan gwamnatin Amurka ga haramtacciyar kasar Isra’ila.

Tattakin ya tattaro daruruwan mahalarta daga bangarori daban-daban na farar hula da na addini, wadanda suka hada da masu fafutuka da masu fafutukar kare hakkin bil’adama, wadanda suka bayyana ci gaba da nuna goyon bayansu ga Falasdinawa da kuma watsi da manufofin yunwa da ake aiwatar kan al’ummar Falasdinu.

Wannan tattaki dai wani bangare ne na jerin zanga-zangar da aka gudanar a wasu biranen Amurka, kamar Collingswood, New Jersey, da Somerville, Massachusetts, domin nuna goyon bayansu ga Gaza, domin fuskantar abin da suka bayyana a matsayin “Killacewa da aiwatar da kisan kare dangi.” Zanga-zangar ta wannan makon dai ta mayar da hankali ne kan goyon bayan matakan kaurace wa shiri da kuma haramta safarar makamai da Amurka take yi zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted