A lokacinda yake tabbatar da cewa shirin makamashin Nukliya na kasar Iran na zaman lafiya ne wanda dukkan wadanda yakamata su san hakan sun sani, to Iran ba zata saurarawa duk wani matsi kan shirin ba don biyan bukatun wasu.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a lokacin zantawa ta wayar tarho da firay ministan kasar Armenia a jiya Asabar. Ya kuma kara da cewa Iran bata damu da binciken hukumar makamashin nukliya ta IAEA ba, don bata da abin moyewa a cikin shirinta.
Ya ce: Har’a yau amfani da karfi ko matsin lamba don hanawa kasarmu hakkinta na amfana da fasahar nukliya ne ba zamu taba amincewa ba.
Dangane da tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya bayan yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka durawa iran da kuma bukatar tarayyar Turai na a koma teburin tattaunawa Pezeshkiya ya bayyana cewa yayi allawadai da Amurka wacce ta kai hare-hare kan shirin nukliyar kasarsa a dai dai lokacinda take tattaunawa da ita, sannan yace kasarsa a ko yawce tana kan tafarkin neman zaman lafiya a yankin.
A nashi bangen Fray ministan kasar Armenia Pashinyan ya ce kasarsa tana alla wadai da HKI da kuma Amurka kan hare-haren da suka kaiwa Iran , wanda hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.