‘Yan tawayen M23 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin Congo

‘Yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta nan take da gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a kasar

‘Yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta nan take da gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a kasar Qatar a wannan Asabar, kamar dai yadda wani jami’i da ke da masaniya kan tattaunawar ya tabbatar wa kafofin yada labarai.

Tsagaita wutar wani bangare ne na ayyana ka’idojin da bangarorin biyu za su amince da su bayan shafe watanni uku ana gudanar da tattaunawar sulhu wadda gwamnatin Qatar ke shiga Tsakani. Yarjejeniyar dai na da nufin rage tashe-tashen hankula da kuma kafa ginshikin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin gabashin Congo  mai fama da rikici.

A cewar jami’in, sanarwar ta kunshi muhimman abubuwa guda uku:  dakatar da yaki nan take, da alkawarin shiga shawarwarin da za a yi, a hukumance cimma cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya, da kuma cimma matsaya kan kafa wasu ka’idoji na tabbatar da tsagaita bude wuta.

Yarjejeniyar ta kuma bayyana taswirar maido da ikon jihohi a gabashin DRC, da zarar an cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe. Ana dai kallon wannan a matsayin wani muhimmin mataki na kawo karshen rashin zaman lafiya da aka shafe shekaru da dama ana fama da shi  a yankin mai arzikin ma’adinai, inda kungiyoyin da ke dauke da makamai suka dade suna arangama da gwamnati har ma da kwace iko da wasu yankuna tare da sarrafa arkin ma’adanar na waddanan a yankuna.

Kungiyar M23 dauke da makamai ta kaddamar da wani hari a cikin watannin Janairu da Fabrairu, inda ta kwace wasu muhimman yankuna a gabashin DRC, ciki har da lardunan Goma da Bukavu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments