Firayim Ministan Australia Anthony Albanese ya yi kakkausar suka game da ayyukan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a Gaza, yana mai kiran rahotannin kashe Falasdinawa a lokacin da suke cikin layin neman abinci da ruwan sha, tare da bayyana cewa wannan ba abu ne da za a iya karewa da kowace irin hujja ba.
A wata hira da ya yi da Kamfanin Watsa Labarai na Australiya (ABC), wanda Kamfanin Dillancin Labarai na Anadolu ya ruwaito, Albanese ya ce ya gabatar da wadannan matsalolin kai tsaye ga jami’an Isra’ila, ciki har da shugaban Isra’ila Isaac Herzog.
Albanese ya ce “Isra’ila na rasa goyon baya ta hanyar ayyukanta, kuma wasu daga cikin ayyukanta ba za a iya kare su ba, yana mai jaddada cewa matsayin Australia kan wannan batu a bayyane yake. “Muna faɗin wannan a matsayin abokai ga Isra’ila: wani lokacin dole ne ku kasance masu kauda kai, wani lokaci kuma hakan ba abu ne mai yiwuwa ba.”
Albanese ya sake nanata goyon bayan kafa kasashe biyu masu cin gashin kansu, a matsayin hanya daya tilo da za ta iya kawo karshen rikici da takun saka tsakanin Isra’ila da Falasdinu, kuma tabbas wannnan zai taimaka wa zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.”
Yayin da yake bayyana irin yanayin goyon bayan da Australia take baiwa Isra’ila, Albanese ya bayyana karara, kan cewa ci gaba da bayar da irin goyan bayan, ya dogara ne ga bin ka’idoji na kasa da kasa. Kalaman nasa sun nuna rashin jin dadin duniya game da yawan mace-macen fararen hula a Gaza da kuma matsaloli na jin kai da Isra’ila ta jefa al’ummar Gaza a ciki.