Cibiyar dake kula da kare hakkin bil’adama a kasar Syria, 9 almirsad) ta fitar da bayani akan rikicin da ya tashi a yakin Suwaida, inda ta bayyana cewa adadin wanda su ka rasa rayukansu sun wuce 1000 a cikin mako daya kawai.
Bayanin ya ce, an kashe mayakan Duruz 336, sai fararen hularsu 298. Haka nan kuma ya bayyana cewa a tsakanin wannan adadin da akwai wasu mutane 194 da jami’an ma’aikatar tsaron gwamantin Syria da na ma’aikatar cikin gida su ka yi wa kisan gilla a bayyane.”
A daya gefen, bayanin cibiyar kare hakkin bil’ada din ta ‘almirsad” ya kuma ce; An kashe jami’an tsaron gwamnatin 342, tare da kuma da larabawan kauye (aBadwu) 21, a cikinsu da akwai wasu uku da ‘yan Duruz su ka yi wa kisan gilla a baina jama’a.
Haka nan kuma bayanin ya ce, wasu jami’an tsaron gwamnatin kasar su 15 sun kwanta dama sanadiyyar hare-haren da sojojin HKI su ka kai wa yankin na Suwaida.
Da safiyar yau Lahadi ne dai gwamnatin Syria ta sanar da cewa an kawo karshen fadan da ake yi a cikin yankin na Suwaidan, bayan da ‘yan Duruz su ka sake shimfida ikonsu acikin birnin, da kuma baza jami’an tsaron gwamnati a kusa da shi.
Kakanin ma’aikatar harkokin cikin gidan Syria Nuruddin al-Baba, ya wallafa sako a shafinsa na “telegram’ cewa: An fitar da mayakan larabawan kauye daga cikin garin na Suwaida, da kawo karshen duk wani fada a cikinsa.
Bayan dakatar da yaki a cikin garin, an kuma aike da kayan agji domin shigar da su cikin garin.