Mataimakin kwamandan sojojin Iran mai kula da tsara farmaki Admiral Mahmud Musawi ya bayyana cewa: Mun yi nasarar samar da sabbin na’urori tare kuma tsofaffin da ake da su, da suke iya yi wa ilahirin samaniyar Iran rumfa daga kowane irin hari na makiya.”
Admiral Musawi ya yi ishara da nasarorin da sojojin jamhuriyar musulunci ta Iran su ka samu a tsawon kwanaki 12 na yakin tsaron kasa mai tsarki.
Bugu da kari Admiral Musawi ya ce; A matakin farko na harin wuce gona da iri da HKI ta kawo wa Iran, ta kai shi ne akan nau’rorin tsinkayo nesa ( radar) da sojojin suke amfani da shi, sai dai duk da haka sojojin Iran sun ci gaba da yaki dare da rana wajen fuskantar abokan gaba.
Haka nan kuma Admiral Musawi ya ce abokan gaba sun yi wa wani sashe na na’urorin tsaron samaniyar Iran illa, sai dai kuma an maye gurbinsu da wasu sabbi an kuma raba su a wurare na musamman.
Bugu da kari Admiral Musawi ya yi ishara da cewa HKI ba ita kadai ce ta yaki Iran ba, da akwai Amurka da Nato da su ka taimakawa mata.
Mataimakin kwamandan sojojin Iran mai kula da tsara farmaki Admiral Mahmud Musawi ya bayyana cewa; Karfin da sojojin Iran suke da shi ne-bisa dogaro da Allah, ya sa ‘yan sahayoniyar su ka kasa fuskantarsu, shi ya sa masu goyon bayansu da kare su su ka rika taimaka musu da dukkanin bayanai, tun gabanin yakin da watanni,musamman Amurka wacce ita ce akan gaba.
Haka nan kuma ya yi ishara da yadda al’ummar Iran su ka dunkule wuri daya domin fuskantar abokin gaba, da hakan ya tabbatar da cewa babu abinda za su iya yi, domin fada da Iran.