Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya ce: Dole ne gwamnatocin Musulunci su tashi tsaye wajen tunkarar ‘yan sahayoniyya
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Hare-haren bama-bamai da aka kai kan dukkanin cibiyoyin tsaron kasar Siriya a cikin ‘yan watannin nan da harin da aka kai birnin Damascus, da kuma mamaye yankunan kasar gami da yunkurin wargaza kasar Siriya, gaskiya ne ta bayyana a fili ga wadancan mutanen da suke tunanin yin biyayya ga wannan karen kazanta zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A jawabin da ya yi a yau Lahadi yayin zaman majalisar shawarar Musulunci, Qalibaf ya bayyana cewa, lokaci ya yi da gwamnatocin kasashen musulmi za su tashi tsaye wajen tunkarar wannan gwamnati tare da goyon bayan al’ummar musulmi domin karya ta.
Ya kara da cewa: A yau ya bayyana ga kowa da kowa cewa makiya sun sha azaba mai zafi daga al’ummar Iran a cikin yakin kwanaki 12 da suka sanya a gaba, kuma babban abin da ya hana makiya cutar da Iran shi ne hadin kan kasa da duniya ta shaida.
Qalibaf ya ce ko shakka babu kiyaye wannan hadin kai shi ne babban aikin da ke kan kowane dan kasar Iran, kuma sharadin wannan hadin kai shi ne daukar Jagoran juyin juya halin Musulunci a matsayin madogara tabbatacciya. Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya bayyana cewa, “Maganganun hikimar da Jagoran ya yi a ganawarsa da jami’an shari’a sun share hanya ga fitattun manyan mutane da sabon fata a tsakanin al’umma.”