Kasar Switzerland ta bayyana matsayinta kan harin da aka kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran
Ministan harkokin wajen kasar Switzerland ya jaddada a wata tattaunawa ta wayar tarho yau da takwaransa na kasar Iran Seyyed Abbas Araqchi cewa: Harin da sojoji suka kai kan cibiyoyin makamashiun nukiliyar Iran ya saba wa dokokin kasa da kasa, yana mai jaddada muhimmancin ci gaba da kokarin dakile tashe-tashen hankula da rashin zaman lafiya.
Ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi da ministan harkokin wajen kasar Switzerland Ignazio Cassis sun gudanar da wata tattaunawa ta wayar tarho, inda suka yi musayar ra’ayi kan ci gaban yankin da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Ministan harkokin wajen na Iran ya yi ishara da hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin ‘yan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan kasar Iran, wanda hakan ya zama cin zarafi ga kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa. Ya kuma jaddada bukatar dukkan kasashen duniya su tashi tsaye wajen yin Allah wadai da wannan karya doka da kuma hukunta masu wuce gona da iri.
Araqchi ya soki matsayin wasu kasashen turai na nuna son kai na tabbatar da munanan ayyukan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da Amurka, yana mai gargadin cewa irin wadannan ayyuka na haifar da lalacewar al’amura da karfafa karya doka da kuma kara ta’azzara rashin tsaro a yankin da ma duniya baki daya.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Switzerland ya tabbatar da goyon bayan kasarsa kan harkokin diflomasiyya, yana mai bayyana cewa a shirye ya ke na ba da duk wani kokari na alheri a wannan fanni.