Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Gana Wa Yara Fiye da Miliyan Daya Yunwa A Gaza

Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da gana wa yara da suka haura miliyan daya yunwa a Gaza tare da ba da umarnin koran al’ummar

Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da gana wa yara da suka haura miliyan daya yunwa a Gaza tare da ba da umarnin koran al’ummar Deir al-Balah daga muhallinsu

Yayin da Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta bayar da rahoton a yau Lahadi cewa: Hukumomin mamayar Isra’ila na fama da kakaba masifar yunwa a Gaza, sojojin mamaya sun ba da sanarwa ga al’ummar Falasdinu da su fice daga yankuna da dama a Deir al-Balah da ke tsakiyar zirin Gaza.

Sanarwar sojojin mamayar ta yi jawabi ga daukacin mazauna yankin kudu maso yammacin Deir al-Balah, a cikin rukunin gidaje 130, 132-134, 136-139, da 2351, gami da wadanda ke cikin tanti a yankin da hanzarta barin gidajensu.

Sanarwar sojojin mamayar ta ce: Sojojinta za su yi aiki da karfin tuwo wajen lalata gine-gine Falasdinawa kamar yadda ta ke ikirari da kuma samar da ababen more rayuwa a yankin, yayin da suke fadada ayyukan da suke yi a wannan yanki domin gudanar da ayyukansu a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments