Rahotanni daga Jahar Zamfara sun ambaci cewa barayin daji sun yi awon gaba da mutanen da sun kai 100, bayan da su ka kashe wasu mutane 9.
Hare-hare irin wadannan a Arewa maso yammacin Najeriya sun zama ruwan dare, ta yadda ba su zama abin yake tayar da hankali a tsakanin mutanen yankin idan ba a wurin dangin wadanda aka sace din ba.
Barayin daji kan kutsa cikin garuruwa da kauyuka suna zakulo mutane daga cikin gidajensu.
Wani da aka yi awon gaba da matarsa ya fada wa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa; Barayin dajin sun kutsa cikin gidansa ne da mislain 11:40 su ka yi harbe-harbe sannan su ka yi awon gaba da maidakinsa.
Wani dan majalisa a yankin Hamisu Faro ya bayyana cewa: wadanda aka sace din sun kai 100.”
A 2021 barayin daji sun yi kutse a cikin wata makarantar kwana ta ‘yan mata,tare da yin awon gaba da dalibai fiye da 300. Daga baya an yi musayar daliban da kudaden fansa da aka biya.
A tsakiyar Najeriya ma, musamman a Jahar Naija, ana samun irin wannan kutse da barayin daji suke yi a cikin kauyuka da garuruwa, mafi yawancin akan babura dauke da bindigogi.
Duk da cewa jami’an tsaro da sojoji suna kai hare-hare daga lokaci zuwa lokaci akan sansanonin barayin dajin, amma ba a kai ga kawo karshen matsalar ba.