Iran Ta Yi Watsi Da Barazanar HKI Ga Cibiyoyin Nukliyar Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da barazanar HKI na kaiwa cibiyoyin makamashin nukliyar kasar don hana kasar abinda take kira makaman Nukliya. Ministan ya kara da cewa kasar Iran zata iya kare kanta ko da Amurka ce ta takaleta, kuma Amurka ta san hakan. Sannan ya ce HKI bata taba […]

Idan Shugaban Kasar Siriya Mai Ci Ya Taka Kasar Iraki Ana Iya Kama Shi

Shugaban kungiyar Asa’ib Ahl-Al-Hak, kungiya mai yaki da yan ta’adda a kasar Iraki, ya bayyana cewa idan shugaban kasar Siriya mai ci Abu Muhammad Al-Jolani ya kuskura ya taka kasar Iraki ana iya tsare shi sabuda gwamnatin kasar Iraki tana da sammashin kama shit un da dadewa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta […]

Sojojin Lebanon Sun Kama Wasu Mutanen Da Suke Shirin Cilla Makamai Kan HKI

Majiyar labarai daga kasar Lebanon sun bada sanarwa kama wasu mutane wadanda suke shirin Cilla Makamai kan HKI. Jaridar Arab News ta yanar gizo ta kuma kasar Saudiya ta bayyana cewa a makon da ya gabata ma an kama wasu mutane wadanda ake zargi da cilla makaman roka kan HKI daga kudancin kasar ta Lebanon. […]

Demokradiyyar Kwango Ta Haramta Jam’iyyar Josept Kabila A Kasar Saboda Hulda Da Yan Tawaye

Gwamnaton kasar Kongo Democradiyya ta bada sanarwan haramta jam’iyyar Josept Kabila tsohon shugaban kasar. Shafin yanar gizo na labarai, Africa News ya nakalto ma’aikatar harkokin cikin gida na kasar tana bada wannan sanarwan. Labarin ya kara da cewa, Josept Kabila ya shugabanci kasar ta kwango har zuwa shekara ta 2019, karkashin Jam’iyyarsa ta ‘the People’s […]

Sharhi:  Kalankuwar  Kona Rayayyu Da Wuta A Gaza

Sojojin mamayar HKI sun fara aiwatar da wani sabon kisa ta hanyar amfani da sabon salo akan Falasdinawa. Kai kace tsawon watanni 18 da su ka dauka suna amfani da makamai mabanbanta wajen kashe mutanen Gaza, bai isha sun cimma manufofin da su ka Sanya a gaba. Sabon salon kisa wanda  ya yi kama da […]

Faransa : Ana tsare da ‘yar Iran saboda goyon bayan Falasdinu

A faransa ana ci gaba da tsare wata ‘yar Iran mai goyan bayan Falasdinu, bis azarginta da iza ta’addanci. Mahdieh Esfandiari (mai shekaru 35) ana tsare da ita tun ranar 28 ga watan Fabrairu, bayan kama ta a binrin Lyon, inda ta ke da zama. Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, […]

Najeriya : Mutum 56 suka mutu a harin Benue

Hukumomi a jihar Benue dake Najeriya sun ce adadin wadanda suka mutu  a harin da ‘yan bindiga suka kai a hukumomin Ukum da Kogo ya kai 56. Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, a wata ziyara a yankin ya shaidawa manema labarai cewa  adadin wadanda suka mutu a harin ya kai 56. ”A yanzu, mutum 56 […]

Hamas ta yi watsi da shirin kwance damara na Isra’ila

Kungiyar Hamas ta yi watsi da kudirin baya bayan nan na Isra’ila na kwance damarar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa domin tsagaita bude wuta a Gaza, tana mai kiran hakan a matsayin wani yunkuri na gurgunta ‘yancin Falasdinu. Tattaunawar da ake ci gaba da yi tsakanin Isra’ila da Hamas ta tsaya cik, inda Isra’ila ta matsa kaimi […]