Kungiyar Hamas ta yi watsi da kudirin baya bayan nan na Isra’ila na kwance damarar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa domin tsagaita bude wuta a Gaza, tana mai kiran hakan a matsayin wani yunkuri na gurgunta ‘yancin Falasdinu.
Tattaunawar da ake ci gaba da yi tsakanin Isra’ila da Hamas ta tsaya cik, inda Isra’ila ta matsa kaimi kan batun kwance damara, yayin da Hamas ta dage kan hakan a matsayin wani muhimmin hakki na kare Falasdinu.
Mahmoud Mardawi na kungiyar Hamas ya jaddada cewa kwance damarar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa abu ne da ba zai yiwu ba.
Ya bayyana kudurin na Isra’ila a matsayin wani dabarun yahudawan sahyoniya da Amurka na kwacewa Falasdinawa karfin kare kansu da kuma tinkarar mamaya.