Shugaban kungiyar Asa’ib Ahl-Al-Hak, kungiya mai yaki da yan ta’adda a kasar Iraki, ya bayyana cewa idan shugaban kasar Siriya mai ci Abu Muhammad Al-Jolani ya kuskura ya taka kasar Iraki ana iya tsare shi sabuda gwamnatin kasar Iraki tana da sammashin kama shit un da dadewa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto shugaban kungiyar Qais Al-khazali yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa jita jitan da yake ji na cewa shugaban kasar ta siriya zai zo iraki a nan gaba, bai taso ba, lokacin zuwansa kasar Iraki bai yi ba saboda zarge-zargen da ake masa tun kafin ya kwace shugabancin kasar ta Siriya, akwai matsalolin doka sosai wadanda za’a fuskanta.
Khazali ya kara da cewa, kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu bai da wata matsala, kuma yana amfanar kasashen biyu, amma zuwansa kasar Iraki a nan kusa yana da matsala, don tun shekara 2014 Jolani shi ne babban kwamnadan HTS, kuma dakarunsa sun yaki dakarunsa a yaki da suka yi da yan ta’adda a lokacin.
Yace bangaren shari’a na kasar Iraki yana cin gashin kansa ne, bangaren zartarwa ba zai hana bangaren shara’a aikinsa ba.
Kafin haka dai firai ministan kasar Iraki Muhammad Shia al-sudani ya hadu da Jolqni a kasar Qatar a cikin yan kwanakin da suka gabata a gaban sarkin Qatar Tamim bin ahli thani