Kasar Rasha Ta Sanar Da Tsagaita Bude Wuta Da Ukraine Na Tsawon Kwanaki Bikin Ester

Gwamnatin Rasha ta sanar da amincewarta da tsagaita bude wuta da Ukraine a wannan karo Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da tsagaita bude

Gwamnatin Rasha ta sanar da amincewarta da tsagaita bude wuta da Ukraine a wannan karo

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da tsagaita bude wuta na kwanaki uku na Ista, inda ya yi kira ga sojojin kasarsa da su kasance cikin shirin ko ta kwana idan Ukraine ta karya yarjejeniyar.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ba da sanarwar tsagaita wuta na kwanaki uku na Ista, yana mai kira ga sojojin kasarsa da su “ci gaba da kasancewa cikin shiri don yiwuwar keta yarjejeniyar tsagaita wutan daga bangaren Ukraine, a sanarwar da fadar Kremlin na fitar.

Putin ya fada a ranar Asabar cewa: “Tsarin tsagaita bude wuta zai nuna a fili gwamnatin Ukraine tana da ikon warware matsalar cikin lumana.”

Putin ya kuma jaddada cewa: A ko da yaushe Rasha a shirye take don warware rikicinta da Ukraine ta hanyar lumana, kuma tana maraba da muradin Amurka, China da sauran kasashe na ganin an cimma daidaito kan batun na Ukraine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments