Hukumomi a jihar Benue dake Najeriya sun ce adadin wadanda suka mutu a harin da ‘yan bindiga suka kai a hukumomin Ukum da Kogo ya kai 56.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, a wata ziyara a yankin ya shaidawa manema labarai cewa adadin wadanda suka mutu a harin ya kai 56.
”A yanzu, mutum 56 ne suka mutu wadanda ba su ji ba su gani ba, da suka hada da iyaye da maza da mata da kananan yara”, in ji shi.
Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar matakai domin kawo karshen hare-hare a jihar.
Gwamnan ya ce tuni gwamnatin jihar ta kara tura jami’an tsaro zuwa yankunan domin kwantar da hankula.
Harin na zuwa ne kimanin mako biyu bayan wasu yan bindiga sun kashe fiye da mutum 100 a wasu hare-hare a jihar Plateau mai makwabtaka.