Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Masu sasantawa Iran a birnin Roma suna da cikakken ikon gabatar da shawara kan matsayin kasarsu
Ali Shamkhani mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi nuni da cewa: Masu gudanar da shawarwari na Iran sun tafi birnin Roma ne domin yin shawarwari karo na biyu da Amurka kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran. Ya ce masu yin shawarwari na Iran suna da cikakken ikon gabatar da shawara kan matsayin kasarsu.
Shamkhani ya yi nuni da cewa: Masu shiga tsakani na Iran suna neman cimma cikakkiyar yarjejeniya bisa ka’idoji guda tara: tsanani, samar da lamuni, dage takunkumi, yin watsi da tsarin Libya/UAE, kaucewa barazana, gaggauta yin shawarwari, dakile masu shirga karya kan Shirin makaman nukiliyar Iran -irin haramtacciyar kasar Isra’ila- da saukaka zuba jari. Iran ta zo ne domin cimma daidaiton yarjejeniya, ba ta mika wuya ga bakaken manufofin Amurka ba.