Ma’aikatar Lafiya Ta Yemen Ta Sanar Da Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada A Hare-Haren Amurka Kan Kasar

Wasu mutane sun yi shahida tare da jikkata sakamakon hare-haren wuce gona da iri da Amurka ta kai kan kasar Yemen Ma’aikatar lafiya ta kasar

Wasu mutane sun yi shahida tare da jikkata sakamakon hare-haren wuce gona da iri da Amurka ta kai kan kasar Yemen

Ma’aikatar lafiya ta kasar Yemen ta sanar a yammacin jiya Asabar cewa: An kashe mutane uku tare da jikkata wasu da dama a hare-haren da jiragen yakin kawancen da Amurka ke jagoranta suka kai a biranen Sana’a, Amran da Ma’arib.

Ma’aikatar ta lafiya ta kara da cewa: ‘Yan kasar Yemen 7 ne suka jikkata sakamakon harin wuce gona da irin da Amurka ta kai kan unguwar Al-Nahda da ke gundumar Al-Thawra, sannan wani dan kasar ya jikkata a gundumar Al-Safiyah sakamakon wani hari da aka kai a makabartar Majel Al-Dama da ke babban birnin kasar, kuma ta yi nuni da cewa “dan kasa daya ya yi shahada yayin da wani kuma ya samu rauni sakamakon harin wuce gona da iri da gwamnatin Amurka ta kai a gundumar Matar’a a gundumar Safiya.”

A yammacin ranar Asabar ne dai dakarun Amurka suka kaddamar da wasu hare-hare ta sama a babban birnin kasar Sana’a fadar mulkin kasar. Sannan jiragen saman Amurka sun kai hari kan unguwar Al-Nahda da ke gundumar Al-Thawra tare da kai wasu hare-hare kan wasu yankuna.

Hakazalika, sojojin Amurka sun kai hari kan makabartar Majil Ad-Dama da ke gundumar As-Safiyah, lamarin da ya yi sanadin jikkata wani dan kasar Yemen. Hakazalika jiragen makiya sun kai hare-hare 4 a yankin Al-Hafa, hari guda daya a kan makabartar Al-Najimat da ke gundumar As-Sab’een, da hari guda 5 da suka kai kan filin shakatawa na 21 ga Satumba a gundumar Ath-Thawra.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments