Bala’in Kogin Congo: Kwale-kwale ya kama wuta, ya kashe mutane 143
A wani mummunan lamari da ya afku a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, akalla mutane 143 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka bace bayan da wani kwale-kwale ya kama da wuta a kogin Kongo da ke arewa maso yammacin kasar.
Akalla mutane 143 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka bace bayan da wani kwale-kwale ya kama da wuta a kogin Kongo da ke arewa maso yammacin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, kamar yadda majiyoyin hukuma suka bayyana.
“An gano rukunin farko na gawarwakin mutane 131 a ranar Laraba, kuma an sake gano wasu 12 a ranakun Alhamis da Juma’a,” ‘yar majalisar wakilan kasar Josephine Pacific Lokomo ta shaida wa kafar yada labaran Faransa.
A nasa bangaren, Joseph Lokondo, shugaban kungiyoyin farar hula na yankin, ya bayar da bayanai kan adadin wadanda suka mutu na wucin gadi, wanda ya kai mutane 145.