Amurka : Ana ci gaba da zanga-zangar kyamar tsare -tsare da manufofin gwamnatin Trump

Ana sake gudanar da manyan zanga-zanga a manyan biranen Amurka a kan nuna adawa da tsare -tsare da manufofin gwamnatin Donald Trump. Masu zanga-zangar na

Ana sake gudanar da manyan zanga-zanga a manyan biranen Amurka a kan nuna adawa da tsare -tsare da manufofin gwamnatin Donald Trump.

Masu zanga-zangar na zargin gwamnatin da keta haddin kundin tsarin mulki da ‘yancin jama’a.

Wannan shi ne karo na biyu a wannan wata da dubban mutane suka yi tattaki a titunan Amurka domin nuna bacin ransu kan yadda Trump ke gudanar da mulkin kasar.

Korafe-korafen masu zanga-zangar sun hada da korar baki daga kasar da korar ma’aikata da gwamnati ke yi da kuma zargin tauye ‘yancin fadin albarkacin baki.

Kazalika masu zanga-zangar na nuna fishi kan irin ikon da Trump ya bai wa Elon Musk, attajirin duniya mai kamfanin Tesla – wanda ya kori ma’aikatan gwamnati sama da dubu 200, ya kuma rushe hukumomin agaji na Amurka da dama a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments