Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana tattaunawar da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, wadda Oman ta shiga tsakani a birnin Roma na kasar Italiya, da cewa an gudanar da shi cikin yanayi mai ma’ana da hangen nesa.
A cikin wata sanarwa bayan tattaunawar, Araqchi ya yi nazari kan yanayin tattaunawar, inda ya bayyana cewa: “Sun gudanar da shawarwari na tsawon sa’o’i hudu a ci gaba da zaman da aka yi a baya, kuma sun samu kyakkyawar fahimta kan ka’idoji da manufofi da dama.”
Ya ci gaba da cewa: An amince da a ci gaba da tattaunawa, da shiga matakai na gaba, da fara taron kwararru. An shirya gudanar da tattaunawar fasaha a matakin kwararru a masarautar Oman daga ranar Larabar wannan makon.