Yeman : Sojojin Amurka sun kai wani gagarumin farmaki kan lardunan Sanaa da Hudaidah

Mutane da dama ne suka mutu sannan wasu sun jikkata sakamakon wasu sabbin hare-hare da jiragen yakin Amurka suka kai kan wasu yankuna na kasar

Mutane da dama ne suka mutu sannan wasu sun jikkata sakamakon wasu sabbin hare-hare da jiragen yakin Amurka suka kai kan wasu yankuna na kasar Yemen.

A daren jiya wayewar yau Lahadi, sojojin Amurka sun kai hare-hare ta sama akalla 20 a Sanaa babban birnin kasar Yemen, da kuma yammacinta da gabashi da kuma kudancin kasar.

Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar Yemen suka sanar a ranar Asabar cewa kimanin mutane 80 ne suka mutu, yayin da wasu 150 suka samu raunuka sakamakon harin da Amurka ta kai a ranar Juma’a a tashar mai na Ras Issa da ke birnin Hudaidah.

Hare-haren na Amurka a Yemen sun kara gurgunta halin da kasar ta Yemen ke ciki.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana matukar damuwarsa game da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, ciki har da hare-haren da aka kai a kusa da tashar ruwan Ras Issa.

Kakakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Stéphane Dujarric, ya bayyana a wata sanarwa jiya Asabar cewa, “Guterres ya damu matuka da hare-haren da Amurka ta kai a ranakun 17 da 18 ga watan Afrilu a ciki da wajen tashar jiragen ruwa na Ras Issa na kasar Yemen, wanda ya yi sanadin jikkatar fararen hula da dama, ciki har da ma’aikatan agaji biyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments