Pezeshkian: Wajibi Ne Kasashen Musulmi Su Kara Karfafa Alakokinsu

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce inganta hadin kai da alaka tsakanin kasashen musulmi da suka hada da Iran da Malaysia na daga cikin abubuwan da ake bukata a halin da ake ciki a duniya. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ta yi da ministan harkokin wajen Malaysia Dato’ Seri Utama […]

Kamfanin Microsoft ya kori ma’aikatansa biyar saboda goyon bayan Gaza

Kamfanin Microsoft ya kori ma’aikata biyar bayan da suka nuna rashin amincewa da kwangilar da kamfanin ya kulla da sojojin Isra’ila. A rahoton cibiyar yada labarai ta Falasdinu, ma’aikatan sun gudanar da zanga-zangar ne a hedkwatar Microsoft da ke Redmond a birnin Washington, sanye da riguna masu dauke da taken nuna adawa da amfani da […]

Shugabannin Guinea-Bissau da Rasha Sun gana a fadar Kremlin

Shugaban Rasha Vladimir Putin da Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo sun tattauna a fadar Kremlin, yayin da ‘yan adawar Guinea-Bissau suka sha alwashin gurgunta kasar gabanin zabe. Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo, sun yi shawarwari a fadar Kremlin, a wani sabon salo na yunkurin da Moscow ke yi […]

Kasashen Habasha da Nijar sun tattauna kan inganta hadin gwiwar soji da tsaro

Ministar tsaron Habasha Aisha Mohammed ta gana da tawagar sojoji daga Nijar karkashin jagorancin ministan tsaro Salifu Modi, inda bangarorin biyu suka tattauna kan yadda za a inganta hadin gwiwar soja da tsaro. Ministar tsaron Habasha Aisha Mohammed ta jaddada cewa; Afirka na da karfin fuskantar kalubale ba tare da tsoma bakin waje ba. A […]

An Fara Tattaunawa Tsakanin Isra’ila Da Hamas Kan Mataki Na Gaba Na Tsagaita Wuta

Kasar Masar ta ce an fara tattaunawa tsakanin Isra’ila da Hamas kan mataki na gaba na tsagaita wuta a Gaza. Ma’aikatar yada labaran kasar Masar ta fada a jiya Alhamis cewa, tawagogin Isra’ila, Qatar da Amurka na birnin Alkahira domin tattaunawa mai zurfi kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. “Bangarorin da abin ya shafa […]

Aljeriya Ta Yi Watsi Da Barazanar Faransa

Kasar Aljeriya ta yi watsi da barazanar da kuma wa’adin da kasar faransa ta gindaya ma ta na cewa za ta soke yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma ta shekarar 1968 wacce ta ba Aljeriya matsayi na musamman. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya ta fitar ta ce “A cikin ci gaba […]

Iran Ta Yi Tir Da Kakkausar Murya Kan Barazanar Soji Da Isra’ila Ke Yi Mata

Iran ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan barazanar soji da Isra’ila ke yi mata, da kuma sukar da kasashen Yamma suka yi kan karfin tsaron kasar a matsayin rashin hankali da wauta. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaeil Baqaei ya bayyana a jiya Alhamis yayin da jami’an Isra’ila ke ci gaba da yi wa […]

7 Oktoba : Sojin Isra’ila Sun Amince Da “Cikakkiyar Gazawa” A Harin Hamas

Rundunar sojin Isra’ila ta amince da “cikakkiyar gazawarta” dangane da harin da kungiyar Hamas ta kai a kudancin kasar a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, wanda ya haifar da yaki a zirin Gaza, bisa sakamakon wani binciken da aka gudanar. A binciken da sojojin Isra’ila suka yi na cikin gida kan abubuwan da suka […]

Habasha Da Somaliya Sun Cimma Yarjeniyoyin Fahimtar Juna A Tsakaninsu

A wani mataki na nuna kara kusanci tsakanin kasashen Somaliya da Habasha, shugaban kasar Habasha Abiy Ahmed ya ziyarci Somaliya. A Shekara guda da ta wuce, kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna. Bayan shafe shekara guda ana zaman dar-dar, a watan Disambar da ya gabata ne a kasar Turkiya, kasashen biyu suka […]