Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta ‘Euro-Med Monitor’ Ta Ce Ta Sami Shaidu Wadanda Suka Tabbatar Da Cewa HKI Tana Azabtar Da Fulasdinwa

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama mai zaman kanta wacce take da cibiya a birnin Geneva na kasar Swizlanta ta bada sanarwan cewa ta sami cikekken

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama mai zaman kanta wacce take da cibiya a birnin Geneva na kasar Swizlanta ta bada sanarwan cewa ta sami cikekken shaidu wadanda suke tabbatar da cewa gwamnatin HKI tana azabtar da falasdinawa wadanda take tsare da su.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana bada wannan sanarwan a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa Jami’an gidajen yari da kuma sojjin HKI suna dukan kawo wuka kan falasdinawa da suka shiga hannunsu, sannan suna azabtar da su sosai, daga ciki har tare da yanke yanke wasu gabban jikinsu.

Kungiyar ta kara da cewa, mutum yana iya ganin alamun duka da kuma kumburan wurare da dama a jikin Falasdiwa.

Banda haka Falasdinawan da aka saka, sun bayyana cewa bayan duka da kuma azabtarwa sojojin HKI sukan hana magunguna ga wadanda basa da lafiya har wasunsu su rasa rayukansu.

Rahoton ya kara da cewa wadannan shaidun sun tabbatar da cewa, HKI tana aikata laifukan yaki, a kan al-ummar Falasdinu sannan alamu sun nuna cewa Falasdinawa da dama sun rasa rayukansu a gidajen yari k kuma wauraren da yahudawan suke tsare da su. Sannan HKI tana buye duk wata shaida da suke tabbatar da irin mummunar mu’amalan da suke yi da Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments