Ministar tsaron Habasha Aisha Mohammed ta gana da tawagar sojoji daga Nijar karkashin jagorancin ministan tsaro Salifu Modi, inda bangarorin biyu suka tattauna kan yadda za a inganta hadin gwiwar soja da tsaro.
Ministar tsaron Habasha Aisha Mohammed ta jaddada cewa; Afirka na da karfin fuskantar kalubale ba tare da tsoma bakin waje ba.
A yayin ganawarta da tawagar sojojin kasar Nijar karkashin jagorancin ministan tsaro Salifu Modi a babban birnin kasar Adis Ababa, Mohammed ta jaddada muhimmancin karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa amincewa da mutunta juna.
Ta sake jaddada aniyar Habasha na tallafawa zaman lafiyar nahiyar da kuma inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka don fuskantar barazanar tsaro tare.
A nasa bangaren, ministan tsaron Nijar ya jaddada cewa, “Habasha babbar aminiya ce wajen inganta tsaro da zaman lafiyar yankin.”
Ya kuma bayyana burin kasarsa na cin gajiyar kwarewar kasar Habasha a fannonin horas da sojoji da inganta tsaro.
Bangarorin biyu sun tattauna kan yadda za a inganta hadin gwiwar soji da tsaro, baya ga wasu batutuwa da bangarorin biyu za su ci gajiyar juna.