Shuwagabannin Afrika ta Kudu, Malasiya da kuma Colombia sun jaddada matsayinsu nah ana jiragen ruwa dauke da makamai zuwa HKI tsayawa a tashishin jiragen Ruwan kasashen su.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ta nakalto shugaban Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa, Firaiministan kasar Malasiya Anwar Ibrahim da Shugaban kasar Colmbia Gustavo Petro suna fadar haka a wani rubutun hadin guiwa da aka buga a mujallar ‘Foreign Policy’ na wannan makon.
Shuwagabannin sun bayyana cewa yakin da HKI ta durawa Falasdinawa a Gaza, ya nuna yadda tsarin dokokin kasa da kasa suna gaza tabbatar da adalci a duniya.
Labarin ya kara da cewa : Ko mu hada kai mu tabbatar da dokokin kasa da kasa, ko kuma dukkan tsaron ya rushe.
Sun HKI ta aikata laifukan yaki a Gaza wadanda suka hada shafi al-umma a doron kasa, inda a cikin shekara guda ta kashe mutane kimani 61,000 tare da taimakon manya-manyan kasashen duniya ko kasashen yamma.
Kasashen Malasiya da Colombia dai suna cikin kasashen da suke goyon bayan karar da Afirka ta kudu da shigar kan HKI a kotun ICC, kuma ya zuwa yanzu kotun ta fidda sammacin kama shuwagabnnin HKI biyu, Wato Firay ministan kasar Benyamin Natanyaho da kuma tsohon ministan yakinsa Aut Galant.
Har’ila yau rubutun shuwagabannin uku ya yi tir da manufan shugaban kasar Amurka ta kwace Gaza ko kuma korar Falasdinawa daga kasarsu.