An Yi Jana’izar Shahidan kungiyar Hizbullah Fiye Da 120 Kudancin Kasar Lebanon A Yau Jumma’a

Shadidan Hizbullah kimabi 130 ne aka yi jana’izarsu a yau jumma’a a kudancin kasar Lebanon. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran tanakalto kungiyar Hizbullah

Shadidan Hizbullah kimabi 130 ne aka yi jana’izarsu a yau jumma’a a kudancin kasar Lebanon. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran tanakalto kungiyar Hizbullah na fadar haka, ya kuma kara da cewa kungiyar ta gabatar da shihidar da dama saboda kare kasarsu, saboda kare kasar Lebanon daga mamayar HKI.

Labarin ya kara da cewa an gudanar da jana’izar ne a garuruwan Aitarun da kuma Aita shaab. Inda mutanen da dam dagayankin zuka halarta . Labarin ya kara da cewa Shahidan sun kai ga shahada ne a hare-haren da sojojin HKI suka kai kan kudancin kasar ta Lebanon a cikin watannin Octoba da kuma Nuwamba na shekara ta 2024.

Labarin ya kara da cewa a yakin dai mutanen leabin kimani 4000 ne suka rasa rayukansu mafi yawansu fararen hula ne wadanda basu san hawa ko sauka ba.

Kafin jana’izar yau ma, sojojin HKI da suke mamaye da wasu wurare a kudancin kasar Lebanon sun yi harbi da bindiga don tsoratar da mutane masu Jana’izar, wanda hakan ya kasance keta yarjeniyar da aka kulla da Ita

A dai dai lokacin ne sojojin HKI ta kashe manya-manyan shuwagabanni da kwamandojojin sojojin Hizbullah na kasar wanda ya hada har da shugaban kungiyar Sayyid Hassan Nasarallah, da magajinsa Sayyid Hashin Safiyyuddiin, wadanda aka yi masu jana’iza a ranakin 23-24 na watan fabarairu da muke ciki a birnin Neirut babban birnin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments