Shugaban Rasha Vladimir Putin da Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo sun tattauna a fadar Kremlin, yayin da ‘yan adawar Guinea-Bissau suka sha alwashin gurgunta kasar gabanin zabe.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo, sun yi shawarwari a fadar Kremlin, a wani sabon salo na yunkurin da Moscow ke yi na kulla huldar tattalin arziki da tsaro da kasashen yammacin da tsakiyar Afirka.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya habarta cewa, hamshakin attajirin nan na Rasha Oleg Deripaska ya halarci tattaunawar da shugabannin biyu suka yi.
Kafofin yada labarai sun ambato wani minista a Guinea-Bissau, ya ce, Kamfanin aluminium na Rasha Rusal yana sha’awar gina layin dogo da tashar jiragen ruwa a kasar, da kuma binciken ma’adanai na bauxite.”
A wani labarin kuma, ‘yan adawa a kasar Guinea-Bissau sun lashi takobin kawo cikas ga harkokin rayuwa a kasar dake yammacin Afirka a yau Alhamis, sakamakon takaddamar da ta kunno kai dangane da wa’adin mulkin shugaba Umaro Sissoco Embalo na shekaru biyar zai kare.
Shugabannin ‘yan adawa sun ce a cewar Reuters, wa’adin Embalo zai kare ranar Alhamis, yayin da kotun kolin shari’a a Guinea-Bissau ta yanke hukuncin cewa wa’adin ta ya kare a ranar 4 ga Satumba.